Page 62
ya dubi Mama Hauwa ransa a bace zai yi magana kenan, ta riga shi. "A'a ai ba ta da laifi, don kawai ta zo ta tunatar da shi cewa Musaddik baida sauran ko Kwandala a gadonsa, don haka idan don Kwadayin dukiyar ya sa zai aura masa ke, to ya fa tuna baida komai, kuma ni ban ga laifinta ba. Don ta yi tunanin hakan, don kowa ma hakan zai dauka, don idan ba hakan ba, ba dalilin aura ma Musaddik ke a irin muguwar rayuwar da ya dora kansa a kai ………? Cikin fusata Malam Mahmud ya daga ma Mama Hauwa hannu ya ce "'Idan ki ka Kara yin magana akan batun da ya shafi Afrah da Musaddik ko auransu ko akan abinda ya danganci Hajiya kilishi Ki rubuta ki aje, zan yi matukar ba ki mamaki, domin zan yi miki abinda mafarkinki bai taba nuna miki zan yi miki ba, zan aje duk wata alaka da ke tsakaninmu, na ci miki mutunci" Mama Hauwa ta bude baki za ta yi magana, ya kara dakatar da ita “kada ki yi min wata magana, ki wuce ki tafi, ki ba ni waje.”
Tabbas Mama Hauwa ta ga bacin rai a fuskar mijinta me tsanani, don haka jikinta ya yi sanyi, a hankali ta juya ta shige dakinta, a yayin da Mallam Mahmud ya dawo da kallonsa ga Afrah wacce take take tsaye kamar an dasata.