Musabbabi Book 1

Page 63

by @yargidanimam

'"Baba abinda Mama Hauwa ta fada gaskiya ne? don zan dauki komai, amma banda wulakanta min kai, don ka fi karfin komai a gare ni,” Mallam Mahmud ya yi dan murmushi cike da kaunar yarsa yace “Hakane Afrah, amma bana son ki sa wannan a ranki balle ya dame ki tunda mu munsan duk abinda muke yi domin Allah mu ke yi kuma dama ai bai kamata Hajiya Kilishi ta so duk wani ci-gaba da Musaddik zai samu ba. Tunda ba ta sonsa ba ta kaunar sa, ba kuma ta kaunar duk wani ci-gabansa, shi kadai ne bai gane hakan ba, yake daukarta a matsayin mai, kaunarsa don haka ko kadan kada ki sa damuwa akan lanarinta”.Afrah ta numfasa tace "Haka ne Baba, amma ci maka mutunci shine abinda zuciyata ba za ta dauka ba". Ya ce "Ki yi hakuri ya ta ki sabar ma kanki kauda kai akan duk wani da zai yi batanci a gareni, musamman haj kilishi wacce zakiyi rayuwa da ita idan kuma ta gane taba ni shine karayar ki shikenan ta samu hanyar kuntata miki Ki sa ma kanki hakuri, kada kuma ki nuna ma kowa, taba ni shine nakasunki, don idan makiyi Ya gano inda lagonki yake, to za ki sha wahala, don ya sami hanyar 6ata miki rai kenan." Afrah ta dan samu natsuwa sannan ta ce “ Na yarda da maganarka Baba, nagode kuma da fahimtar da ni da ka yi". Ya yi murmushi ya ce “Badamuwa. Ki je ki yi sallah, ni ma masallaci zan tafi,