Page 64
ga shi can ana shirin tayar ma da sallar." Ta gyada kai, lokaci daya ta wuce zuwa dakinta, domin ta aje jakarta ta makaranta,. Zuciyarta cike da tsanar Hajiya Kilishi. Domin duk wanda zai taba mata mahaifi, to ba ta da makiyin da ya fi shi.
Karfe daya da rabi na rana Hajiya Kilishi ta tsayar da motarta a kofar gidan Hajiya Rakiya, lokaci daya ta janyo wayarta da ke dore a saman motar, ta dannan ta kira wayar Hajiya Rakiya. Bugu daya ta dauka kamar ta na jira "Hajiyar Allah.”, ta fada cike da zumudi, Haj kilishi ta amsa "Ga-ni a kofar gidanki, ki yi sauri ki fito don Allah da sauri tace “Toh, ga-ni nan fitowa yanzun nan" Mintina uku tsakani Hajiya Rakiya ta fito a gaggauce, ta bude gaban motar da sauri ta shiga, bata jira komai ba ta harba titi, Sun yi tafiya me nisa, sun fito daga cikin garin Minna har zuwa wata yar karamar rugar fulani, kafin su karasa rugar. Hajiya Kilishi ta tsayar da motar, suka fito da Kafa suka Karasa rugar. A dai-dai gaban wata Yar Karamar bukka suka tsaya, gaba dayansu. Hajiya Kilishi ta ce “ Ahuwonka”daga cikin bukkar aka amsa “lale, shigo daga ciki”, nan da nan suka cusa kai cikin bukkar, wani bafullatani ne mara kyan gani a zaune akan wani buzu, Gabansa duk tarkace ne na kayan tsubbu, yana ganin Hajiya Kilishi, ya washe baki, ya hau fara'a, ya ce.