Musabbabi Book 1

Page 65

by @yargidanimam

"'Ashe Hajiya ce?" Ita ma ta yi dariya ta ce "Nice Mai Rakwacam!” Bayan sun zaunane, Mai Rakwacam ya bukaci jin abinda ke tafe da Hajiya Kilishi, ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ido cikin ido, Sannan tace “Na zo hankalina a tashe ne Mai, Rakwacam Akan maganar MusaddiK ne, aure zai Yi,ni kuma ko kadan ba na bukatar ya yi auren, domin auransa zai iya zama hanya ce ta arziki, kuma hanya ce da za ta iya kai shi ga samun canjin rayuwa. Ni kuwa ka fi kowa sanin duk wani ci-gaba na Musaddik ba na maraba da shi, kuma Yarinyar Yar-uwarsa ce ta can dangin mahaifiyarsa, auransu ina da tabbacin zai Kara kusanta shi da dangin Mahaifiyarsa wanda kasan bana son hakan tun farko,”Mai Rakwacam ya dubeta ya ce "Yanzu me kike bukatar ayi Haj “ Ta muskuta ta kara lankwashe kafafunta Ta ce "Kamar yadda ka saba taimaka min kuma na ke ganin haske, shine na zo gareka, abinda na ke bukata, shine a lalata Maganar auran, kada ya yiwu, a bata komai da Komai a bar shi a yadda yake, ya ci-gaba da gararambarsa ta lalacewa kowa ya daina ganinsa da wata daraja” Mai Rakwacam ya janyo wani katon tulu ya shiga surkullansa, ya dauki tsawon lokaci yana aikin tsubbunsa, sannan ya dago ya kalleta, Yana girgiza kai, muninsa ya kara fitowa,sannan ya ce.