Page 66
"A gaskiya Hajiya kin san tsakanina da ke babu cuta babu cutarwa, ba na kuma boye maki duk wani abu da na gani na dadì ko na rashin dadi don haka maganar auran Musaddik babu abinda zai hana shi yiwuwa, sai dai mutuwar daya daga cukinsu”, Hajiya Kilishi ta dafe Kirjinta, hankalinta ya tashi matuka ta ce "Yanzu babu wata hanya da Za’a bi a dakile lamarin, dole sai hakan ta faru?" Ya jinjina kai yace “Kwarai kuwa Haj . Dole sai wannan auran ya kasance, babu wata mafita, idan kuma ba ki yarda ba, to ki je duk inda za ki je, amma ki sani, kudinki za su ci a banza babu biyan bukata” Hajiya Kilishi ta kalli Hajiya Rakiya, duk jikinsu a sanyaye, sannan Hajiya Kilishi ta dawo da kallonta ga Mai Rakwacam ta ce "Na yarda da maganarka, ban kuma kasance me jayayya akan duk abinda ka fada ba, domin ina ganin gaskiya a cikin aikinka, sai dai abu daya" Ya dubeta yace “Menene shi?"' Ta ce "Na saduda akan auran, tunda banda wata mafita amma ina son Musaddik ya dawwama akan halin da yake ciki, ko kadan ba na son a sami wani canji a game da rayuwarsa a dalilin auransa". Ya yi dariya yace "Wannan ai babu canji, ko na yi aiki akai ko ban yi aiki akai ba, ba za'a samu wani canji ba.