Page 67
Zai ci-gaba da zama a halin da yake ciki, auransa ba zai canja shi da komai ba” Hajiya Kilishi ta ce "Godiya na ke" ta balle jaka ta fito da kudì ta mika masa, ya amsa yana godiya gami da kara karfafa mata guiwa akan lamarin Musaddik, daga nan suka yi masa sallama suka fito.
Har sai da Hajiya Kilishi ta fara tuka mota, sannan Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “Amma yarinyar da za ta auri Musaddik mahaukaciya ce ko?" Hajiya Kilishi ta ce "Ko daya da hankalinta ras, tasan abinda take yi”
''To idan ba mahaukaciya ba, me za ta ci da Musaddik, wane jindadì za ta samu daga gare shi mutumin da ina ganin ko wanka ba ya yi, Kullum yana wurin *yan daba yana shaye-shaye, yana kuma yawon bangar siyasa, ko dai suna tunanin za su sami kudi ne a hannunsa?" Ta girgiza kai ta ce "Ubanta ya fi kowa sanin Musaddik baida ragowar sisin kwabo, ni dai ban 'san dalilin da mahaifinta yake son hada wannan auran ba da zai zama masifa da fitina ga yarsa dama shi mutum ne me kafiyar tsiya, amma 'tabbas ba na son Musaddik ya auri *Yarsa Afrah" Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “To ki na ganin za mu gwada sa'ar wani wajen ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Hajiya. A gaskiya na yarda da aikin Mai Rakwacam, kin fi kowa sanin cewa