Page 68
duk shekarun nan, shine yake taimaka min, bai taba yi min aiki na ga rashin sa' ar aikin ba. Idan kuma abu ba zai yiwu ba, zai gaya min, ba zai cin min kudi a banza ba, na kuma sha gwada wani wajen, idan ya ce ba zai yiwu ba. Haka nan za'a ci min kudi kuma babu biyan bukata, shi ya sa yanzu idan ya gaya min abu ba Zai yiwu ba, na kan hakura gaba daya na rungumi kaddara, kamar yanzu da na saduda na hakura akan maganar auran nasu” Ta nisa gami da hadiye yawu kafin ta ci-gaba da magana. Hajiya Rakiya ta ce “ kina da gaskiya, tunda kin yarda da shi, gara ki aje hankalinki waje daya, domin tabbas ya iya aiki”, Haj kilishi cikin fuska me cike da bakinciki tace “Hakane, amma nayi alkawarin bazan taba barin Afrah ta samu kwanciyar hankali ba,dole zansa auran ya fita a ranta da kanta zata nemi wajen gudu in dai nice”, Haj Rakiya ta yi dariya tace “ kin ji ki da wata magana za ki bata ma kanki lokaci, dai kawai domin rashin kwanciyar hankali, har ya wuce wanda mijinta Zai sakata a ciki? Halinsa kadai ya isa ya sa ta gudu ta bar shi, wa zai iya da Musaddik” Hajiya Kilishi ta yi dariya ta ce "Kai Hajiya Rakiya sai a barki, kuma fa hakane” Gaba daya suka kwashe da dariya . Sai dai fa ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, domin har cikin zuciyarta auran nan yana daya daga cikin binda ta tsana a duniya, amma babu yadda za ta yi, tunda haka kaddara ta riga fata, sosai take jin tsanar Afrah a cikin zuciyarta da mallam mahmud.