Page 69
Ta Bangaren gidan Malam Mahmud kuwa shirye- shiryen bikin Afrah da Musaddik ya kankama, ita kuwa Na’ima tunda ta dawo gidan, take ma Allah godiya daya gajarce mata wahalar auran. Musaddik . Inna Halima da kanta ta sai ma Afrah gado da katifa da sauran tarkacen kayan kicin. Kudin kuma da su Kabir suka ba mahaifinsu a matsayin gudunmuwa, su ne ya ba Inna Halima ta sayo kujeru kayan kallo da firij har da keken dinki da sauran duk kayan da ake bukata. Duk da haka sai da kudin suka ragu, su ne ya yi amfani da su ya sayi kayan abinci. Mama Hauwa kuwa tunda ta fahimci Mansur da Kabir ne suka bada makudan kudin sayayyar Afrah, ta ji bakinciki kamar ya kasheta, don sai da ta Kirasu ta yi masu kaca-kaca. Ta nuna masu matukar bacin ranta.
Shirye-shirye sun yi nisa, sun kankama, amma ga Afrah, al'amarin ya fara ba ta tsoro , saboda tun daga ranar da Musaddik ya zo gidansu suka Yi magana, bai kara dawowa ba. Ba shi, ba labarinsa, dan ko, ta je gidan Inna Halima ranar juma'a har ta gama kwanakinta ta dawo gida, ba zai zo ba. A zahiri abin yana damunta, tana matukar son ta san halin da yake ciki Ga shi ba ta san inda za ta same shi ba, balle ta neme shi ta ji lafiyarsa. Haka zalika bata nuna damuwar komai a gaban kowa