Page 70
Musamman mahaifinta da Inna Halima, haka Zalika ko yaushe tana samun karfin guiwa daga Ya Sayyadi Habib tare da addu'o'"i, wadanda a yanzu su Afrah ta rike suka zamar mata garkuwa. Idan ma akwai abinda ke damunta, to bai wuce habaici da maganganu marasa dadi da Mama Hauwa ke mata ba, tare kuma da nuna mata tana cikin jin dadi, don ganin rayuwarta za ta lalace, a dalilin auran Musaddik, amma da yake ba ta son damuwar mahaifinta, haka ta dage tana hadiye duk abinda Mama Hauwa ta yi mata ba tare da ta nuna damuwarta ba, don bata son mahaifinta ya dauka tana damuwa ne akan zata auri musaddik wanda ita zuwa wannan lokacin ta riga ta sa ma kanta auran musaddik bata jin wata damuwa a yanzu.
Har yau daya rage saura kwana shida daurin auran Musaddik da Afrah, da yamma Afrah na cikin wankin ragowar kayanta, gefe mallam Mahmud ne zaune tun dazu, da alama wani yake jiran zuwansa, dai-dai lokacin Musaddik ya yi sallama ya shigo.Afrah ta yi saurin dago da kanta tana kallonsa, ko don ta dade ne ba ta gan shi ba? Sai ta ga yayi baki, ya rame duk bakinsa ya bushe kamar wanda ya shekara bai sha ruwa ba, tausayinsa ya Kara kamata, amma shi kallo daya ya yi mata, ya dauke kansa ya wuce wajen Kawunsa, ya tsuguna a gabansa, da kayansa duk sun yi datti ya gaishe shi Malam Mahmud ya dade yana Kure masa da ido cike da tausayawa, babu abinda bai saka a zuciyarsa ba, musaddik kyakkyawa me farar fata yau dubi yadda ya koma idan ba kyakkyawan sani kayi masa ba tabbas ba zaka iya gane shi ba a yanayinsa na yanzu.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM