Musabbabi Book 1

Page 71

by @yargidanimam

Mallam Mahmud ya numfasa yace “ina ka shiga kwana biyu,duk inda yakamata na nemeka na nemeka amma baka nan, haka kuma wayarka itama bata samuwa, lafiya kake ko?” Musaddik Ya dan numfasa, sannan ya ce "Kawu kasan idan zabe ya gabato bama samun zama, na dan kwana biyu ma bana garin, wayata kuma ta samu matsala sai da na gyarata

Mallam Mahmud ya girgiza kai yace "Yanzu Musaddik don Allah ba za ka yi ma kanka fada ka fita daga harkar nan ba, bangar siyasa ba ta dace da kai ba, kana sane da irin wahala da zubar da mutunci da ku ke yi akan mutanen da su kansu ba su san darajar kansu ba balle darajarar ku, ya kamata ace ka natsu ka san inda duniya ta sa gaba." Musaddik ya dan sosa keyarsa ya ce “Sai hakuri Kawu, ayi ta mana addu'a dai har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana agaji, a kara hakuri da mu don Allah “ya gyada kansa Cike da damuwar data riga ta zamar masa jiki yace “Allah ya kyauta ya kuma shiryaka” Ya gyara tsugunnansa ya ce yana fadin "Amin” Malam Mahmud ya dube shi ya ce “Kana Kirge da kwanakin da suka rage na auranku ko ?”ya gyada kai alamar eh, sannan ya ci-gaba da magana '"To shine dalilin nemanka, akan maganar wajen da za ku zauna, ka na da wajen da za ku zauna dunne ko kuwa babu ?" Musaddik ya zame ya zauna sosai a kasa ba tare da ya damu da kurar dake kasan ba, yace “ Eh kawu,nayi magana da Haj shekaranjiya, ko zata taimaka min da aron gidan da zan zauna, ko da nawa ne na da da na zauna da Hannatu