Page 72
sai ta nuna min ai ba ta da iko da gidan, tunda na Hannatu ne, ba nata ba” Ya dan yi shiru. Sannan ya dora da cewa “Shine ta ce sai dai ta taimaka min da daki anan cikin gidan namu, na kuma amince da hakan, tunda banda sauran wani zabi, sai dai ban sani ba ko Afrah ba zata so zama tare da ita ba” Malam Mahmud ya yi shiru na dan wani lokaci, sannan ya dago da idonsa ya kalli Afrah da take ta wankinta tamkar ba ta jin abinda suke fada a hankali ya dawo da kallonsa ga Musaddik, sannan yace
"To shi kenan, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri. Allah kuma ya daidaita zaman da ita, domin nasan Afrah bata da wani jayayya akan hakan” musaddik ya kara risinawa ya na cigaba da yi ma kawunsa godiya har sai da ya dakatar da shi. Daga nan Mallam Mahmud ya tashi ya shiga cikin dakinsa, a nan ne Musaddik ya juya yana kallon Afrah, ita ma ta juyo ta kalle shi, fuskarta dauke da murmushi, cikin jin nauyinta ya dauke idonsa a kanta. Zuciyarsa cike da mamakin irin zuciyar Afrah, ya kamata ace ta yi fushi da shi, a dalilin rashin kara waiwayarta da bai yi ba, amma babu alamar damuwar hakan ko tsanarsa akan hakan. Dai-dai lokacin da Malam Mahmud ya fito rike da kayan sawa. Mama Hauwa ta fito daga daki ta tsaya ta kama kugu ta rike tana kallonsu. Mallam Mahmud ya zauna, Sannan ya mika ma Musaddik kayan, shaddoji ne da yadiddika masu kyau, akalla zasu kai kala bakwai yace “ Nasan babu abinda ka tanada na game da komai na hidimar bikin