Page 73
don haka ga kayan sawa nan, sannan ga wannan”Ya mika masa Naira dubu goma yace “Bance kaje ka kashesu a banza ba, ko kaje ka sha wani abun da su ba, na umarceka da ka aje su ka yi amfani da su a bikin ko wata harkar ta alheri”. Ya karba cike da godiya da yabo, ya yi ta godiya Malam Mahmud yana fadin. "Ka daina yi min godiya, don ban ga dalilin yi min godiya ba, kai fa dana ne don na yi maka wani abu, babu bukatar ka yi min godiya." Musaddik ya ce "Kawu karamcinka a gareni, ya kai duk inda ya kai, godiya ba za ta isa ba. Sai dai na ce Allah ya kara girma."Mallam Mahmud zaiyi magana kenan Mama Hauwa ta amshe. "Ai dole ka ce godiya ba za ta isa ba, gata mugun abu, aka ce inji wanda bai samu ba, Yanzu wanda zai kawo kayan lefe, shi ake ba Kayan sawa, wannan aure shine gallafiri, tunda na ke ban taba ganin irin wannan auran gatan ba.ta juya ta kalli Afrah tace “ lalle Afrah ba zaki taba yin daraja a wajen musaddik ba, don baisan darajarki ba, balle tsadarki, daga sama kawai ya sameki”, Malam Mahmud ya daga mata hannu, ransa a bace yace “Na gaya miki, na Kara gaya miki, ki fita daga cikin duk abinda ya shafi auran Afrah, babu ruwanki, ki shiga taitayinki, na rantse idan kika kaini bango za’ayi auran nan bakya cikin gidan nan” , a hankali ta saki tsaki