Musabbabi Book 1

Page 74

by @yargidanimam

tace, a yayin da take shigewa dakinta "Kanku ake ji, ni meye nawa, iyakar mu ido” ta karasa shigewa daki harda turo kofa tana cigaba da maganganunta a hankali. Malam Mahmud ya dawo da kallonsa ga Musaddik, wanda fuskarsa ta nuna matukar damuwa da maganganun da Mama Hauwa ta fada, yace “Kada ka damu Musaddik Hauwa ce fa haka take, ba za ta taba canjawa ba, don haka babu dalilin da mutum zai damu da dabi'unta, kai ma ina umartarka da ka manta da duk zantukanta”, ya jinjina kai yace “ Hakane kawu, babu komai, nagode” Daga nan Musaddik ya hada kayansa a cikin leda, wanda zuwa lokacin Afrah ta gama abinda take yi ta shige dakinta, ranta da hankalinta a tashe da maganganun da Mama Hauwa tayi. Wanda hakika ta san gaskiya ne. Duk abinda ta fada, ba ta da wata daraja a wajen Musaddik Ko ba'a kan rashin tsinana komai akan bikin ba, Ko a cikin zuciyarsa, ta san ba ta da daraja, domin daga dukkan alamu. Musaddik baya sonta dole zai aureta, don Kawunsa, kamar yadda dole za ta aure don mahaifinta.

Malam Mahmud ya riga Musaddik fita daga gidan, don a tunaninsa zai tsaya su tattauna da Afrah, ita ma Afrah ta yi tunanin zai nemeta su yi magana, musamman akan auran nasu, duk da ta san ba wani shirye-shiryen da za su yi akan auran amma ga mamakin Afrah, mahaifinta yana fita.