Musabbabi Book 1

Page 75

by @yargidanimam

MusaddiK ya tattara kayansa shi ma ya fice, ba tare da ya nemeta ba, ko ya shigo dakinta sunyi magana ba.Shin wane irin aure za ta yi? Me Musaddik ya dauketa?”, wadannan tambayoyin Afrah tana matukar bukatar amsar su., amma ba ta san inda za ta samo amsarsu ba.

Saura kwana uku daurin auran. Afrah ta nemi hutu a Islamiyyarsu, a ranar Ya Sayyadi ya nuna matuKar damuwarsa na rabuwa da yarinyar da zuciyarsa take muradi. Iya yadda ya so ya boye damuwarsa a yau, hakan ya faskara, yadda idanun Afrah suke fitar da hawaye, haka idanunsa suka yi ta tsiyayar hawaye shi ma masu matukar dumi da kyar ya samu ya lallashi kansa Sannan ya ci-gaba da yi mata nasiha gami da shawarwari a game da zaman auranta da za ta fara da Musaddik, wanda ta ji dadin nasihohinsa, domin tasan tabbas za su taimaketa. Daga bisani ya ba ta wata takarda a matsayin gudunmuwarsa. Ta karba ta yi godiya kwarai, wanda sai da ta isa gida ta zauna, sannan ta san abinda Ya Sayyadi Habib ya ba ta a matsayin gudunmuwarsa, kudi ne kimanin Naira dubu talatin . Ta kara tausaya ma Ya Sayyadi, ta kuma kara tausaya ma kanta da wannan auran Kaddarar daya gitto rayuwarta. Hakika ba za ta taba mantawa da Ya Sayyadi ba, kuma ba za ta taba daina yi masa addu' ar samun mace wacce ta fita komai ba.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR lMAM