Musabbabi Book 1

Page 76

by @yargidanimam

mace ta-gari ba, wacce ta fi ta komai. Ta dade tana tunanin yadda za ta yi da kudin, domin dai ba zata iya kai ma mahaifinta kudin ba, don ba ta son ya san cewa akwai wani da namiji da take so a cikin rayuwarta Don ba ta son ta sa masa damuwa na tunanin ya hanata abinda take so. Ya hada ta da abinda zuciyarta ba ta taba so ba, don haka ta adana, Kudin ta Boyesu da kyau da tunanin bayan bikinta za ta san abinda za ta yi da su.

Washegari daya kama sauran kwana biyu daurin auran. Inna Halima da yayyin Afrah, Naja' atu da Sakina da 'yan-uwan mahaifiyar Afrah su biyu su ne za su je su yi ma Afrah danki, amma kafin su tafi, sai da Malam Mahmud ya ja kunnan Inna Halima akan duk abinda Hajiya Kilishi ta yi masu, kada su biye mata, ko su tanka Su yi abinda ya kai su kawai, su dawo, domin ya san Hajiya Kilishi, ya san halinta. Inna Halima ta yi masa alkawarin babu abinda zai faru, daga nan suka dunguma tare da motar kayan zuwa gidansu Musaddik. Amma ga mamakin Inna Halima, sai ta ga Hajiya Kilishi ta yi masu kyakyawar tarba har da lafiyayyen girki, wanda ya ji nama, ga lemo kala- kala, ga sakin fuska da suka samu. Wannan lamari ya ba Inna Halima mamaki,domin bata taba zaton haka ba, hakanan kuma ta ji bata samu nutsuwa da hakan ba. (Boys Quarters),