Musabbabi Book 1

Page 77

by @yargidanimam

Haj Kilishi ta ba Musaddik mai dauke da dakuna biyu da bandaki, sai kicin, an yi ma Afrah dankinta, dai dai karfinsu daki ya yi kyau matuka, Domin ita kanta Hajiya Kilishi ta yi mamakin irin kayan da ta ga an malala ma Afrah. Babu makusa. Hakika Malam Mahmud ya yi matukar kokari, wai ma ina ya sami kudin daya fitar da Afrah kunya? Domin dai ta san bai aje ba, bai ba wani ajiya ba. Bayan komawarsu gida, cike da jin dadì da farin-ciki Inna Halima ta ba Malam Mahmud labarin irin karamcin da Hajiya Kilishi ta yi masu. Wanda shi ma ya yi mamaki, ya kuma ji dadi tare da addu'ar Allah ya sa har cikin zuciyarta ta gyaru, ta kuma amshi auran Afrah da Musaddik da zuciya daya. Ita ko Mama Hauwa a lokacin da Naja'atu ta gaya mata irin kyakyawar tarbar da suka samu a gidansu Musaddik, gaba daya sai ta ji bakin-ciki da 6acin rai ya cika zuciyarta, ko kadan ba ta so hakan ba, domin bata faran Afrah ta samu sassauci ko dadin aure ko yaya ne, tayi zaton Haj kilishi ta zabi zama da su Afrah waje daya ne ai sabida ta kuntata mata, amma kuwa yadda tasan bakin halin Haj kilishi anya dagaske take ta amince da Afrah?.ko kuwa dai wani tuggun ne.

Sai washegari wanda ya rage saura kwana daya daurin auran, sannan Musaddik ya zo ganin Afrah, shi da wasu abokansa guda hudu marasa kyan gani, don da ganinsu ka san shaye- shaye ya gama da su, banda wari ba abinda suke yi, hakan yasa Afrah ba ta dade a wajensu ba, ta yi karyar za