Musabbabi Book 1

Page 78

by @yargidanimam

ta koma ta karasa aiki. Haka suka tafi babu wani abin arziki Afrah na komawa gida, ta shige daki ta kulle kofa ta shiga rusar kuka tamkar ranta zai fita, ba ta taba ganin irin wannan auran ba, wanda miji da mata duk ba sa dokin sa, auran da Ko kawarta daya ba ta gayyata ba, auran da ko dan-kwali miji bai kawo gidansu a matsayin lefen ta ba. Anya kuwa ta yi ma kanta adalci? Na karbar auran Musaddik? Sai dai ta Bangaran zuciyarta daya tana kara karfafa ma kanta guiwa akan auran don ba don farin-cikinta za ta yi ba, don Farincikin mahaifinta* za ta yi, kuma biyayya ce tasa ta sadaukar da farin-cikinta ga mahaifinta, don haka tana addu'ar Allah ya ba ta ikon cinye wannan jarabawar, ta kuma sa a ranta zata jure komai har zuwa lokacin da burin mahaifinta zai cika akan musaddik, tausayin musaddik kuma zaisa ta kara jurewa da halayensa ko da bata sonsa. Ta tashi ta goge hawayenta, ta bude kofa ta fita, ta je ta dauro alwala ta shiga gabatar da sallolin nafila , domin samun natsuwar zuciya da Kuma yayewar bakin-ciki. Dai-dai agogo ya nuna karfe daya da kwata na dare. Afrah na kishingide kan darduma, tun bayan da ta gama nafilolinta, barci ya kwasheta. Malam Mahmud ya tura kofar ya shigo a hankali, gami da sallama, ya dan jima tsaye a kanta yana kallonta, kafin ya kira sunanta. A gaggauce Afrah ta tashi ta zauna tana kallon mahaifinta.