Musabbabi Book 1

Page 79

by @yargidanimam

"Ki natsu Afrah, magana zan yi da ke". Ya fada a lokacin da yake zaunawa a gefen , katifarta ita ma ta gyara zamanta sosai , tana kallonsa. tace “To baba” - Malam Mahmud ya numfasa cike da tsantsar damuwa, ya zuba mata ido, sannan ya . fara magana”Na kwanta, amma barci ya kasa kwashe ni, iya yadda na ke boyewa tare da danne darnuwata a 'wannan daren, na kasa, domin damuwata tafi ta kullum kasancewar gobe ita ce ranar da zan rabu da ke, itace ranar da za ki kafa sabuwar rayuwa a wata duniyar, da baki sababa” Ya kara nisawa, sannan ya dora da cewa "Ina matukar kaunarki fiye da duk yayan da na haifa a dalilin ke ma kin fi su kaunata, na kuma fi samun kulawa da mutuntawa daga gareki. Afrah ina son ki sani, har ga Allah ba irin auran da na ke kwadayin ki yi kenan ba, Kamar yadda ba mijin da na ke miki mafarkin ki aura ba kenan, amma babu yadda za mu yi da Kaddara da kuma abinda Allah ya hukunta a kan mu Afrah ina son ki sa ma ranki cewa auranki da Musaddik jihadi ne, ki kuma sa a ranki cewa kin yi domin Allah ne, domin kuma taimakon rayuwar dan-uwanki.sannan ibada zaki je yi gidansa” Hawayen idanun Afrah suka balle ta shiga zubar da hawaye, tamkar an bude famfo. Malam