Musabbabi Book 1

Page 80

by @yargidanimam

Mahmud ya muskuta, damuwarsa ta kara yawa a hankali ya ci-gaba da magana cikin rawar murya “Afrah na rokeki don girman Allah ki yi hakuri da dukkan hali da dabi 'un Musaddik, na san ba mutumin kwarai bane a yanzu, sabanin da amma muna da tabbacin da ikon Allah halinsa na da zai dawo gare shi, ki yi hakuri, ki yi juriya, sannan daga Karshe ina rokonki da ki yafe min Afrah ki yafe min” da sauri Afrah cikin kuka mai karfi tace,

“Haba Baba me ya sa'ka ke neman gafarata? Babu komai, na riga na daukar ma kaina yi maka biyayya akan duk abinda ka ke so, na kuma yi imanin cewa Allah zai taimakeni, na cinye wannan jarabawar. Kuma can a allon kaddara ta , babu sunan kowa a matsayin mijina, sai Yaya Musaddik, saboda haka na karbi wannan kaddarar da hannu biyu”. Malam Mahmud cikin sanyin jiki ya kara duban Afrah, yace “Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira,Allah kuma ya tabbatar da alheri a cikin rayuwarki da ta aurenki, Allah yasa wannan auran ya zama sanadiyyar dawowar musaddik hanya madaidaiciya”. Wannan addu’o’in sa mahaifinta ke mata yana daya daga cikin abinda ke karfafa mata guiwa tare da jin tana samun nutsuwa a zuciyarta. ta dube shi cike da kauna ta ce "Amen Baba, na gode sosai”, daganan ya yi mata sallama, ya tashi ya tafi, jikinsa a matukar sanyaye, yana fita ta kara rushewa da kuka tayi ta kuka har ta ba uku lada. Hakika dole ta sa ma kanta hakuri da dangana, domin ba za ta taba ba mahaifinta kunya ba, zata yi iya yinta domin cika masa burinsa, a wannan daren gaba daya ta aje dukkan burikanta a gefe.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM