Musabbabi Book 1

Page 81

by @yargidanimam

tasan babu so ko kaunar musaddik a cikin zuciyarta ,amma tayi alkawarin za ta ba shi dukkan kulawa da Kariya a gare shi, za kuma ta yi zama na so da kauna tunda babu wanda ke da ikon ganin zuciyarta balle asan bata son sa, sannan kuma za tayi zama na mutuntawa da Musaddik, za kuma ta dauke shi shugabanta, kamar yadda addini musulunci ya tanadar, don baida nutsuwa bazai bata lasisin wulakanta shi ba tare da muzanta shi ba.

Washegari kuwa Karfe biyu da rabi alkawarin Allah ya cika akan Musaddik da Afrah, domin Kuwa an daura auransu a kofar gidan Malam Mahmud akan sadaki Naira dubu arba’in kacal! Wanda shi ma ba tare da sanin kowa ba shi ya biya kudin sadakin.

Bayan daura auran. Afrah ta ci kuka har ta gaji, musamman da Inna Halima ta shigo dakin nata, ta sa ta gaba da nasihohi da shawarwarin yadda za ta zauna da Musaddik. Har zuwa lokacin da za°a kai ta dakinta, wanda abin takaici hatta motar da za'a kai ta dakin mijin nata, da motar yayan ta Mansur aka , kaita Inna Halima da su Naja'atu da matar Mansur Sai dangin mahaifiyarta su uku su ne suka kai Afiah dakin mijinta, nan ma Hajiya Kilishi ta yi kokarin wadata su da abinci har suka bar gidan ba su yi kuka da komai ba. Inna Halima kuma addu’a take yi Allah yasa Haj kilishi ta dore akan wannan sabon canjin da ta samu rana tsaka.

Sun tafi sun bar Afrah ita kadai. Da kanta ta tashi ta zazzaga dakin nata, hakika ta yaba ma mahaifinta, domin dai dakinta ya kawatu, kamar na kowace *yar gata, tabbas an fitar da ita kunya