Musabbabi Book 1

Page 82

by @yargidanimam

Bayan ta gama ganin ko'ina ne, ta dawo ta zauna tana tsammanin shigowar angon nata. Amma shiru, har zuwa lokacin da agogon bangon ta ya buga karfe daya na dare ba Musaddik, babu alamarsa, ta tashi cikin matukar damuwa ta kulle kofar dakin, sannan ta wuce bandaki, ta dauro alwala, ta kyautata niyyarta ta shiga yin sallar nafila, zuciyarta cike da tsantsar danuwa Afrah ba ta gushe tana sallah ba, har sai da aka fara kiran sallar farko na asubah, dai-dai lokacin Afrah ta ji ana bugun kofa da Karfin gaske, tamkar za’a balle Kofar, ta mike a gigice zuwa bakin kofar tana kokarin sanin ko waye. "Afrah ki bude kofar” muryar musaddik ta daki dodon kunnenta, da sauri ba tare da tunanin komai ba ta bude kofar, tana budewa, ya fado dakin a buge yake, koda Afrah bata san warin giya ba, to tabbas Musaddik tsami da warin giya yake, da sauri ta matsa, ya fada kan doguwar kujera yana sambatun surutai.wanda bata gane ko kalma daya da yake fada ba. A sanyaye ta maida kofar ta rufe, ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallonsa, hawaye na malala daga idanunta, ya dago da idanunsa jajir! wadanda ba su iya buduwa duka, ya ce "Kin tsaya a kaina, ki matsa ki bani waje” • Da sauri Afrah ta koma kan daya kujerar ta zauna, tana goge hawayenta Da kyar ta samu ta tashi ta yi sallar asubahi, wanda kafin ta idar musaddik ya gama wanke