Musabbabi Book 1

Page 83

by @yargidanimam

Kasan dakinta da aman giya, me matukar wari, tana idarwa, ko addu' a ba ta gama yi ba, ta tashi ta shiga aikin goge aman, tana kuka me dauke da sautin ban tausayi. Bayan ta gama gyara wajen ne,ta taimaka masa ta janye shi daga falon zuwa uwardaka. Ya bata wandonsa da fitsari, ya bata rigarsa da amai duk da tana cike da jin nauyinsa, haka ta taumaka masa wajen cire kayansa, ta sa masa wasu , sannan ya koma kan gado da kansa, ya kwanta, cikin rashin cikin rashin dawowa hayyacinsa . Bayan ya kwanta ne. Afrah ta fice ta koma falonta, ta zauna ta dasa wani sabon kukan, gaba daya har jikinta ya yi dumi, shin wace irin mummunar rayuwa ta shigo a daranta na farko a gidan mijinta? Ba ta fara da komai ba, sai da aikin kwasar aman dan giya da aikin gyara wajen fitsarinsa, shin haka rayuwarta za ta kasance tare da Musaddik? Idan ko har haka ne rayuwarta ta riga ta kare babu sauran wani abu na farin-ciki ko na jin dadì da ya rage à gareta. Kaiconta, kaicon wannan mummunan rayuwar, hakika ta yi sadaukarwa me girma, a yanzu ne kuma ta fahimci ba karamin aiki bane a gabanta, duk yadda take tunanin abin ya wuce nan,lalle dole ta karfafama kanta guiwa,

Karfe takwas Afrah ta yi wanka, ta gyara kanta, sai dai kallo daya za ka yi mata ka san tana cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa, domin kuwa har ta rame idanunta sun zurma ciki, fuskarta ta yi fauu! Idanunta ma'abota girma da