Page 84
haske, duk sun kankance, a sakamakon kukan da ta yi, har zuwa lokacin Musaddik barci yake yi ko motsi ba ya yi, ta leka shi yafi a kirga amma kwance yake tamkar matacce.
A dalilin hakan Afrah ta janyo hijabinta ta sa ta fito zuwa cikin gidan, domin ta gaida Hajiya Kilishi. A katon falonta ta tadda ita zaune da me aikinta Amimi, tana ta kaiwa da komowa wajen shirya abincin karyawa akan tebur, cikin sallama Afrah ta shiga falon Hajiya Kilishi. Ta dago ta kalleta gami da amsa sallamar can cikinta. Har kasa Afrah ta zube tana gaida ta cike da girmamawa da mutuntawa. Hajiya Kilishi ta amsa ba yabo, ba fallasa, rai a bace kamar wacce aka yi ma wani laifi, hakan ko ya ba Afrah mamaki, Domin sanda aka kawota gidan a jiya, ba haka ta karbeta ba, ta karbeta cikin kyautatawa da kauna, to mènene yanzu? Me ya yi zafi? Za ta ga irin wannan canji nan da nan, ko daman Hajiya Kilishi tana da dalilinta na yin duk abinda ta yi a baya ne? "Ya kwanan amarci?" Tambayar Hajiya Kilishi ta katse Afrah daga tunanin da take yi, ta dan kalleta kadan, ba tare da ta ba ta amsa ba. Hajiya Kilishi ta ci-gaba da cewa "Na san kin yi kwanan amarci me dadì, domin ina da tabbacin angon naki ya ba ki kyakkyawar kulawa da dawowa akan lokaci dai-dai sallar asubah, na san kuma ya zo maki da kyakkyawan sakamakon kaiwa asubah a waje, kinsan abinda yasa yakai wannan kokacin a waje , nasan kuma kin fahimci cewa mace bata gaban musaddik, abinda ke gabansa kenan wanda idanunki suka ganar miki”.