Musabbabi Book 1

PAGE 85

by @yargidanimam

Cike da mamakin maganganunta. Afrah ta dubeta idanunta sun kada sun yi jajir! Hajiya Kilishi ta gyara zamanta gami da yi mata wani sakaran kallo, sannan ta ce “Afrah na yi mamakin da ki ka amince da auranki da Musaddik a matsayinki na yarinya mai natsuwa, mai kuma ilimi, na yi zaton za ki yi kokarin girmama kanki, ki samu rayuwa ta-gari, wacce za ta amfaneki ta kuma amfani yayanki, wadanda zasu so samun uba nagari, sai ga shi kin buge da watsa ma kanki rayuwa da kanki. Meye riba ko amfanin auranki da mutumin da bai san inda rayuwarsa tasa gaba ba, me zaki tsinta?”

Ta kara kura mata ido ta ci-gaba da cewa. "Shi mahaifin naki daya hada auran ku, ya san cewa Musaddik bai dace da ke ba, idan kuma don abin duniya ya aura miki shi. Ya san cewa Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, asalima inda ku ke zaune yanzu, a matsayin alfarma ce, taimaka maku na yi, alfarma nai maku, na ba shi aron wajen da ya aje ki. Idan na so sai na ce ya je ya nemi wajen zama, amma na taimaka masa, domin Allah." Anan ne Afrah ta dago da idanunta, da tuni suka fara zubar da hawaye ta ce "Mahaifina bai taba tunanin ya aura ma Yaya Musaddik ni sabida tunanin fanshewa daga wani abin duniya daga gare shi ba…………..

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan Imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM