Page 86
ya aura ma sa ni ne, saboda Allah ya riga ya rubutani a cikin matan da Yaya Musaddik zai aura Ita kuma Kaddarar Ubangiji babu wanda ya isa ya kauce mata, don haka a shirye na ke da na karbi Kaddarar, zan kuma rike Yaya Musaddik da daraja fiye da tunanin me tunani, zan zamar masa majingina “ Hajiya Kilishi ta saki tsaki ta ce "A hakan har wace daraja Musaddik yake da ita? Ke kam! Ki na da babban aiki a gabanki, na zama da dan iska, dan giya a matsayin miji" Afrah ta yi dan murmushi ta ce "Ba komai. Allah ya ba ni ikon ci-gaba da zama da shi a hakan domin ta nan zan sami aljannata”. Tana gama fadin hakan, ta mike, ta ce "Dama na zo na gaisheki ne, bari na koma, kada ya tashi barci ba na nan” Tana gama fadin haka ba ta saurari komai ba, ta fice, a yayin da Hajiya Kilishi ta bi ta da wani mugun kallo, zuciyarta a zafafe, lallai yarinyar nan zuciyarta a dake take, yanzu duk abinda musaddik ya yi mata a jiya ba ta gani ba? Mai-gadi ya tabbatar mata da cewa sai asubah ya dawo gida, kuma ya dawo a buge da giya, ace ango ya yi ma amaryarsa haka a daren farkonsu ai ya isa dalilin da za ta nemi kashe auran ma, amma kalleta ko a jikinta. Hmm! Rashin sani, ya fi dare duhu, domin Hajiya Kilishi ba ta san dalilin auran