Page 87
Afrah da Musaddik ba kenan, don ya sami me taimaka masa, tare da tallafa masa da kuma Kokarin maido da shi hanya madaidaiciya, don haka duk halayensa ba baki bane agun Afrah, ta sani, asalima halayen nasa su ne suka sa ta aure shi . Afrah na shiga daki, ta tadda Musaddik zaune a bakin gado, ya yi tagumi hannu biyu, tana ganinsa a haka, ta yi saurin korar damuwar da ke fuskarta cike da fara' a, ta karasa inda yake, ta ce “ ka tashi kenan”, ya dago fuska cike da damuwa mara misaltuwa, ya kalleta a hankali cikin matsananciyar kunya, ya dauke kallonsa daga gareta, sannan ya ce. "Afrah don Allah ki yi hakuri, ki yi min afuwa “ - Ta dan yi murmushi ta ce "'Me ka yi da ka ke ncman afuwata?" Ya numfasa ya ce "Kin fi kowa sanin abinda na yi, domin ko ni da na yi, sai dai na kintaci abinda na yi, na tuna, dan abinda zan iya tunawa amma sanin komai, sai ke da na yi a gabanki, don haka ki yi hakuri, koma me na yi a daran jiya, ina neman yafiyarki, don Allah"ta jinjina kai tace "Ya wuce, babu komai, amma kasan wani abu?” Ya so ya kalli cikin kwayar idonta amma sai yaji bazai iya hada ido da ita ba, ya girgiza kai yace “A’a” Afrah ta dan gyara tsayuwarta tace "Ina yi maka kallon me ilimi wanda ya san abinda Allah ya fada akan giya da kuma me shanta, ban taba tunanin zan