Page 88
tadda kai a cikin shaukin shan giya ba, bayan ka san giya ita ce uwar kaba’irai Komai za ka iya aikatawa, idan ka sha giya, to me zai sa ka sha, me zai sa ba za ta zama abar tsana a gunka ba, sai dai abar kauna, sannan ka rasa lokacin da za ka sha, sai a daren auranka yaya Musaddik? Me ya sa za ka yi min haka?, ko ya ya ne ba zaka iya hakuri ba ko da a wannan daren ne, da nake bakuwa a gareka”. Musaddik ya runtse idanunsa, ya bude, sannan ya ce "Ba za ki taba ganewa ba Afrah, ba za ki gane ba, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa na ke tsoron aurenki, ba zaki gane komai ba a yanzu, ni nasan yadda nake ji”
Yana gama fadin haka, ya mike yana kokarin shiga bandaki. Ya na kauda kansa a dalilin baya son taga hawayen da yake kokarin boye mata. Afrah ta yi kokarin maida hawayenta, jikinta ya yi sanyi tayi saurin cewa “yakamata ka fara yin wanka ne kafin kayi sallah, bari na kaima ruwan wankan” A hankali musaddik ya dawo da baya, ya koma ya zauna a bakin gadon, ya sadda kansa kasa,a yayin da Afrah ta yi gaggawar fita, ta hada rishonta, ta dura Kananzir wanda harda shi a cikin kayan da aka kawota da su.ta kunna ta dora masa ruwan wanka, cikin kankanin lokaci ruwan ya yi zafi, ta juye ta kai masa. Ya yi wankan, ya yi kuma alwala , bayan ya fito ne ya kintsa ya yi sallar asubah. Dai-dai Karfe tara da rabi zuwa lokacin ta gama abin karyawa. Domin Malam Mahmud ya yi kokarin hado Afrah da garar abinci, hatta garin tuwo, sai da ya hadota da shi. Musaddik yana gama karyawa bai saurari komai ba ya fice duk da abincin ma kadan ya ci.
Ko kadan babu dokin auran a ransa, balle har ya yi tunanin ya zauna a gida na dan lokaci tare da matarsa. Haka ya tafi ya bar ta cikin matsananciyar