Musabbabi Book 1

Page 89

by @yargidanimam

damuwa. Domin duk yadda ta dauki abinda sauki Ta ga ba haka bane, hakika akwai katon aiki a gabanta, ta ko wane bangare.

WAIWAYE, ADON TAFIYA.......

Alhaji Mansur Musaddik Mai Fata shahararre ne, kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya mallaki manya- manyan kamfanoni na sarrafa fatu, sannan bayan hakan yana safarar fatun zuwa kasashe makwaftan Nigeria. Hakan ya sa kasuwancinsa ya kara fadada, ya kuma sami karbuwa sosai, mutum ne me saukin kai, me addini tare da son kyauta ma 'yan’uwansa, duk da ya taso cikin matsananciyar tsana ta Yan uba a dalilin maraicin uwa da uba da ya yi gaba daya, amma duk da haka bai hana shi taimaka musu ba, bayan da Allah ya zabe shi a cikinsu ya azurta shi. Haj kilishi itace matarsa ta farko,auren saurayi da budurwa. Haj kilishi macece me ji da kanta, fadin rai da daukar kanta wani abu, tana da karfin izza, gata da matsanancin kishi, wanda hakan yasa take ganin Alhaji Mansur ba zai iya yi mata kishiya ba, musamman idan ta yi la'akari da irin son da yake mata, da kuma bai taba nuna mata yana da sha’awar wata ya mace ba bayan ita, ko sha’awar ya kara aure ba, shi yasa ta mike kafa take shimfida iko da mulki.ta haifa masa 'ya' ya har uku duk mata Hassana da Hussaina, sai Amina. Bakincikinta daya a rayuwarta, shine yadda bata da da namiji, ga haihuwar ta tsaya mata, ta tashi hankalinta wajen ganin likita da son ta cigaba da haihuwa amma likita ya tabbatar mata lafiyarta kalau haihuwar ce dai kawai Allah bai kawo ba. Wannan al’amari ya kara tada hankalin haj kilishi domin tana da