Page 90
gamshahshen sanin cewa babu abinda mijinta yake so yake kuma nema ido rufe irin magaji da namiji, saboda yana kwadayin ya samu mataimaki a lokacin da karfinsa ya kare, jikin Haj kilishi ya fara sanyi, damuwa ta fara mata yawa, tunaninta na mijinta va zai iya mata kishiya ba ya fara canjawa.don haka kullum addu'oi 'nta. Allah ya ba ta haihuwar da namiji, amma ba ciki ba dalilinsa, Hakan ya sa a lokacin da Alhaji Mansur ya furta mata maganar Karin auransa da Harirah hankalinta ya yi masifar tashi, hauka ne kawai ba tayi ba, haka zalika ta yi Kokarin lalata auran ta hanyoyi da dama. Domin ta yi ta asarar kudinta a wajen Malamai da Bokaye, don dakatar da auran. amma da yake Kaddararran al'amari ne. Allah ya riga ya Kaddara Harirah sai ta kasance uwar dan Alh Mansur, sai da Allah ya tabbatar da auransu. Sai dai Harirah ta zauna cikin kunsar bakin- cikin Hajiya Kilishi, domin kuwa ta kankane komai a gidan. Harirah ba ta da wani karfi a matsayinta na matar gida, komai sai Hajiya Kilishi ta amince, ta kuma sa baki sannan yake yiwuwa. Koda ta bangaren Mai-gidan ne, domin Hajiya Kilishi ta riga ta gama mallake shi ta hanyoyin sihirinta. Hakan ya sa Harirah ta ci-gaba da zama a wulakance a kaskance a gidan mijinta. Har zuwa lokacin da Allah ya yanke mata wahala, ya dubi hakurin da ta yi a dalilin cikin da ya bata, tunda ta sami cikin, kadarin Hajiya Kilishi ya Karye, domin yadda Alhaji Mansur ya dauki son duniya ya dora akan cikin, tamkar ba’a taba yin ciki a gidansa ba sai akan Harirah.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI BISMILLAHIR RAHMA NIRRAHIM