Musabbabi Book 1

Page 91

by @yargidanimam

ga kuma kyakkyawar kulawa da take samu daga gare shi, wannan lamari ya fi komai tayar ma da Hajiya Kilishi hankali. Musammam da ta fuskanci da gaske Harirah ciki, gareta don haka ta ci-gaba da asarar Kudinta a wajen Malamai, domin a lalata cikin Harirah Amma ina. Alkawarin Allah baya tashi. Komai tayi a banza, cikin Harirah ya ci-gaba da girma da kuma samun kulawa. Haj kilishi ta cigaba da zama cikin dar dar da fargabar kada Harirah ta haifi da namiji. Har zuwa lokacin da cikin ya isa haihuwa. Da yake Allah ya riga ya rubuta Harirah ba za ta rayu da danta ba, ya sa tana haihuwar dan, Allah yana daukar ranta, ga koshi, ga kwanan yunwa kenan! Alhaji Mansur na murnar samun abinda ya dade yana addu'ar samu, ga tashin hankalin rashin matarsa, uwar dansa daya tilo daya fara samu. Wacce yake sa ran za ta kula masa da dansa har zuwa girmansa. Ya shiga tsananin tashin hankali, irin rashin kyautatawar da ya ke yi ma Harirah a da ya yi ta dawo masa yana ta da masa hankali, ya so Harirah ta rayu ko don ya jiyar da ita dadin da bai jiyar da ita ba a baya.

Ta Bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ba Harirah ta so ta rasu ba, dan da ta haifa ta so ya rasu, domin tana ganin duk duniya ba ta da wani bala'i sama da shi.don haka don Harirah ta rasu, ai ta barta da masifa tamkar an kashe maciji ne , ba a sare kan ba Rasuwarta ba wata fa'ida a gareta, gaba daya tsanar dan da Harirah ta haifa ya gama ratsa Jinin jikin Hajiya Kilishi, ko kadan ba ta kaunarsa. Hankalin yan’uwan Harirah yafi na kowa tashi adalilin rashin yar’uwa da su kayi da kuma tunanin yadda dan Harirah zai rayu ba tare da mahaifiyarsa ba.