Musabbabi Book 1

Page 92

by @yargidanimam

Tunaninsu kuma ya kara karkata akan waye zai dauki Musaddik ya rike shi, ya raine shi kamar yadda uwa zata raini danta.Inna Halima wacce ita ke bin Harirah a haihuwa, da yake kuma shekarunsu ba wani tazara bane sosai, ya sa tare aka yi masu aure. 'Inna Halima kuma ta rigata haihuwa da makwanni hudu, danta ita ma namiji ne, mai suna Abdullahi, don haka ta roki Alhaji Mansur da ya bata Musaddik ta hada da Abdullahi ta shayar da su. Alhaji Mansur ya yi farin-ciki matuka, ya kuma sami dimbim natsuwa ya kuma kalli Inna Halima a matsayin maganin matsalarsa, kuma mai taimaka masa akan gudan jininsa Musaddik dan da yake jin kamar ba shi da kowa duk duniya Sai shi. Dan da yake jinsa har cikin jinin jikinsa, wannan shine dalilin da ya sa Inna Halima ta dauki Musaddik ta hada shi da danta da ta haifa. Wanda ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, ta so Musaddik a bar shi ya tagayyara ne, da rashin nonon uwa, har' shi ma ya bi uwar ta sa, amma sai ga shi ya sami wata uwar wacce take da tabbacin zata bashi kulawa kamar yadda mahaifiyarsa zata ba shi ko ma fiye da haka, domin yan’uwan Harirah suna daya daga cikin yan’uwan da bata taba ganin zurfin zumunci irin na su ba, ga shi dai basu da yawa sai shegiyar zuciya da hadin kai kamar kashin awaki.