Page 93
Bayan "yan watanni, lamarin ya fara kwanta ma Hajiya Kilishi, musamman da yake ba ganin Musaddik take ba, ta kuma mallaki hankalin Mijinta waje daya, domin baya sha'awar ya kara wani auran. Amma abu daya ya ci-gaba da nukurkusar zuciyar Hajiya Kilishi tare da hanata samun, sukuni shine ganin irin yadda Alhaji Mansur yake matukar kulawa da Musaddik. Domin hatta gadon da zai kwanta, sai da ya saya masa, kaya kuwa na sawa na alafarma yake saya masa, duk wani abu da ake ma da dan gata, to fa shi yake ma Musaddik, kuma kullum kwanan duniya, in dai yana kasar , to duk aikin da ke gabansa, sai ya ture ya je ya ga Musaddik sau uku safe rana da daddare, hakan ya sanya shakuwa tsakaninsa da dansa. Su kansu su Inna Halima rikon Musaddik ya amfanesu sosai, tunda mijinta ba shi da wani, Karfi don haka Alhaji Mansur ya dauke shi ya ba shi aiki a daya daga cikin kamfanoninsa, wanda ake yin takalma, sannan kuma shine ya rushe gidansa, ya Kara gina masa sabo dai-dai da rayuwar dansa. Wannan lamari ya tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, dalilin da ya sa kuma kenan ta tsani Inna Halima, domin ta sha nikar gari ta je har gidan ta ci mata mutunci ta kuma kirata da makwadaiciya , tun tana shanyewa har ta gaji, ta gaya ma Alhaji Mansur.