Page 94
Wanda hakan ya yi sanadiyyar da suka sami sabani da Hajiya Kilishi. Ya yi mata kaca-kaca, ya kuma gargadeta da kada ta kara taka gidan Inna Halima da sunan cin mutunci, idan kuma ta Kara to ta shaida a bakin auranta. Hakan ya sa dole Hajiya Kilishi ta hakura da zuwa gidan Inna Halima, ba don ta so ba, ko don ta daina jin zafinta ba, sai don tana son igiyar auranta da take tunkaho da ita, sai dai ta cigaba da bin bokaye da malamai domin a raba soyayyar da ke tsakanin Musaddik da mahaifinsa, ta kashe kudi ba iyaka, amma bata dace ba, ko ya yi kamar ya kama sai kuma ya karye. Ta rasa yadda zata bulloma al’amarin.
Shekarun Musaddik biyar , ya fara makaranta wacce ta masa sunanta, a lokacin ne kuma Haj Kilishi ta fara sa kahon zuka tare da tusa ma Alh Mansur son ya amshi Musaddik ya dawo hannunsu Amma Alhaji Mansur ya ki daukar hudubarta, domin ya fi kowa sanin halinta, yana da tabbacin Musaddik ba zai taba jin dadin zama da ita ba. A haka a daddafe har Musaddik ya kammala firamare, cikin kyakkyawan yabo da sakamako, ga kyakyawar tarbiyyar daya samu daga uwar rikonsa ,halinsa na hakuri da son mutane ya kara taimaka masa wajen cikar kamalar rayuwarsa. Musaddik tun yana yaronsa, kyakyawa ne sosai me cikar kamala, kwarjini ga farin-jini.
Burin Hajiya Kilishi bai cika ba na raba Inna Halima da Musaddik har sai da Musaddik ya kai aji hudu na sakandire, sannan Alhaji Mansur da kansa ya zauna da Inna Halima da mijinta Malam Saminu da kuma Malam Mahmud mahaifin Afrah, ya