Page 95
bukaci zai maida rikon dansa hannunsa, ya Kuma yi masu godiya a bisa rikon da suka yi ma marayan dansa. À ranar Inna Halima ta yi kuka har hawayenta suka Kare , domin ta shaku da Musaddlik tana kuma Kuma Kaunarsa fiye da ya' yanta da ta haifa, babu wanda bai tausaya mata ba a cikin wadanda aka yi zaman da su. Alhaji Mansur ya ba Inna Halima da mijinta da Malam Mahmud kyautar kujerun makka, tare da kudi masu tsoka, domin ya yi ikirarin ba shi da wanda suka fi masa 'yan-uwan Harirah, Domin su ne suka taimake shi akan dansa a lokacin da yake bukatar taimako, kuma ba zai taba mantawa da 'Yar-uwarsu Harirah ba, wacce ta ba shi abinda zuciyarsa ke shaukin samu, ta kuma rasa ranta a dalilin hakan. Wannan karamci da Alhaji Mansur ya yi masu, ya ba su sha'awa sun kuma yi masa godiya sosai, sai dai kamar yadda Inna Halima ta shiga damuwa akan rabuwa da Musaddik, haka shi ma Musaddik din ya shiga matsananciyar damuwar rabo da Mamansa, ya yi kewarta, ya yi kuka mai tsanani, amma ba shi da yadda zai yi, domin haka Allah ya Kaddara ma rayuwarsa.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM