Page 96
Komawa da rayuwarsa gidan mahaifinsa ya fuskanci bambanci matuka na kulawar uwa abinda ya saba Inna Halima na yi masa, na nuna Kauna tausayi da soyayya, sam ba haka ya riska a gidan mahaifinsa ba. Daga matar ubansa, domin babu abinda yake fuskanta sai tsana da tsangwama daga Hajiya Kilishi. Amma a bayan idon mahafinsa, domin a gaban idonsa, duk duniya babu me kima da mutuncin musaddik a gun Haj kilishi.domin takan nuna duk duniya babu wani abin da take so sama da shi. Hakan ya sa Alhaji Mansur ya sami natsuwa, domin a tunaninsa Hajiya Kilishi ta canja halinta, tana zaune da dansa domin Allah akan mutuntawa. Shi kam Musaddik masifar tsoron Hajiya Kilishi yake yi, don haka ko a cikin tunaninsa. Bai taba tunanin ya gaya ma mahaifinsa halin da yake ciki da Hajiya Kilishi ba, sai dai idan abin ya dame shi, ya kwaso jiki zuwa gidan Inna Halima da kukansa ya na gaya mata. Amma ko ta yi kokarin ta je ta gaya ma Alhaji Mansur, sai Musaddik ya hanata, a Cewarsa baya bukatar duk wani abu da zai tayar da hankalin mahaifinsa, don haka idan tana son farin-cikinsa, to kada ta gaya masa komai, har kullum Inna Halima tana sha' awar halin Musaddik na damuwa da farincikin wasu fiye da farin-cikinsa. bata da yadda zatayi tunda tana bukatar kwanciyar hankalin musaddik, sannan kuma bata son ta shiga lamarin gidan Alh mansur, a kokarin ta na tsira da mutuncinta a wajen Alh mansur din.
Haka lamarin ya ci-gaba har zuwa lokacin da Musaddik ya kammala makarantar sakandire,