Musabbabi Book 1

Page 9

by @yargidanimam

inda Alhaji Mansur ya yanke shawarar kai Musaddik kasar waje, domin ya samu Digree dinsa a can,Tashin hankali! Hajiya Kilishi ta samu matukar damuwa akan hakan, shin wace irin kulawa ce Musaddik yake samu fiye da "ya 'yanta, wadanda tuni suna ma'aura, ko wacce na gidan mijinta. ita shi kenan ba ta da wani abu da za'a kyautata masu, kamar yadda Alhaji Mansur yake kyautata ma musaddik Me ya sa ya fi son Musaddik akan kowa? Ko don shine Magajinsa? Ita shi kenan haka za ta tashi a tutar babu? A gaskiya Musaddik ya zamar mata fitina, yanzu har kasar waje zai je ya yi karatu domin idonsa ya Kara budewa.yasan "yancinsa, ya gagareta ya kuma buwayi rayuwarta. Duk hanyar da za ta bi, don ta kawo cikas akan kai Musaddik kasar waje, ta bi, amma ba ta sami nasara ba.don tuni Alh mansur ya samo masa gurbin karatu a oxford university dake london.Haka zalika ba a dauki wani dogon lokaci ba, aka gama komai. Alhaji Mansur da kansa ya dauki Musaddik zuwa London, bai dawo ba sai da komai ya yi dai-dai. Watau ya tabbatar da Musaddik ya fara shiga aji,sannan ta dawo Nigeria kan kasuwancinsa a yanzu ji yake ya mallaki komai na duniya, tunda yana da babban da namiji kamar