Musabbabi Book 1

Page 98

by @yargidanimam

Musaddik,wanda zai iya daukar nauyin kasuwancinsa, zai iya kula masa da dukiyarsa, shi ya sa yake kokarin ba shi ingantaccen ilimi da zai amfane shi. Ya kuma amfani rayuwarsa. baida fargabar komai a yanzu, koda mutuwa ya yi.

A yayin da Hajiya Kilishi kullum take kwana take tashi da tunanin, yadda za ta yi da, Musaddik domin ta dauke shi a matsayin shine matsalar rayuwarta. Musaddik ya dage wajen mutunta rayuwarsa a London, ya rike mutuncinsa, duk wata harka, idan ba ta arziki bace, ba za ka taba ganinsa a ciki ba, ya rike addini da al'adarsa, abinda ya kai shi, shi yake yi, ya maida hankalinsa sosai wajen karatunsa domin ya riga ya fuskanci abinda mahaifinsa ya fi bukata kenan a duniya Don haka ba zai taba ba shi kunya ba, zai tsaya ya yi abinda ya kamata. Dalilin hakan Musaddik sai da ya zama (Best Student), saboda tsananin hazakarsa .cikin haka har ya kammala Digree dinsa, ya kuma dora Masters dinsa, sau uku kawai ya taba dawowa Najeriya. Sai dai Alhaji Mansur da yake kokarin ziyartarsa akai-akai, har ya kammala Masters dinsa ya tattaro ya dawo gida Najeriya, ya zama nagartaccen matashi me kwarjini da cikar kamala, ga kyakkyawan hali abin koyi ga kowa.