Page 99
Dawowar Musaddik Najeriya bayan kammala karatunsa. Alhaji Mansur ya sami cikar burinsa, gaba daya ya ji ya gama mallakar duk wata ni’ima ta duniya, mako uku da dawowarsa. Aka yi gagarumin bikin ba shi kamfanin yin siminti na Alhaji Mansur daya mallaka masa, ya kuma mallaka masa katafaren gida, da mota. amma wannan. karon sai da Hajiya Kilishi ta yi bore akan ba za ta taba yarda da wannan hukuncin ba. Domin ita ma 'ya' yanta da ta haifa ai 'ya' ya ne, ganin yadda ta tada hankalinta, ya sa akan dole ya sai ma 'ya'yanta motocin hawa, duk da suna gidan mazajensu, sannan ya mallaka musu makudan kudade domin su tsaya da kafafunsa.hakan ne kawai ya sassauta mata damuwar da take ciki. Sai dai tana ganin lokaci ya yi da za ta dauki Kwakkwaran mataki akan Musaddik. A lokacin ne kuma Alhaji Mansur ya bukaci Musaddik ya fito da mata, ya yi masa aure. Domin cikar kammalarsa, domin duk a rayuwarsa abinda ya rage ya yi masa kenan, ya cikasa rayuwar dansa, shi kam! Musaddik ba shi da wata mace da yake so, asalima shi bai taba tsayawa ya yi soyayya da ko wace mace ba. Ko da ya je gidan Inna Halima ya gaya mata abinda mahaifinsa ya umarce shi da yi, shawara kawai ta ba shi akan ya tsaya ya nemo ma 'yayansa uwa ta-gari, don haka ya yi taka-tsantsan! wajen nemo matar aure.