Page 100
Domin zai iya yiwuwa macen ta so shi domin abinda ya mallaka ko don gidan daya fito ko don kyau da cikar kamalarsa. Tabbas! Maganar Inna Halima gaskiya ce. Ya zamar masa dole ya tsaya ya nemi abokiyar rayuwa ta-gari.
A yayin da gefe daya Mama Hauwa ta fara yi ma kawun musaddik Malam Mahmud maganar mai zai hana Musaddik ya zo ya nemi 'yarsu Sakina, ayi tuwona maina.tunda tana ganin ya isa da Musaddik din yana cewa ya ba shi sakina shikenan, domin tana kwadayin yarta ta samu gidan hutu gidan arziki irin gidan Alh mansur.
Nan da nan Malam Mahmud ya gargadeta akan kada ta fito da maitarta a fili, idan Musaddik yana son Sakina, da kansa zai furta. Tunda ai gidan ba bakonsa bane, yana zuwa yana kuma. ganinta, Don haka idan yana sonta, ba sai an yi masa magana ba, da kansa zai furta, hakan yasa dole Mama Hauwa ta yi shiru da maganar. sai dai ta dora Sakina a hanyar ta dinga nuna ma Musaddik so da kulawa a duk sanda ya zo gidan, har ya 'Fahimci inda ta dosa, Amma abinda Mama Hauwa ba ta sani ba, shi ne tuni Hajiya Kilishi ta gama shirinta tsaf akan kokarinta na farko na ganin ta tarwatsa rayuwar Musaddik.Domin zuwa wannan lokacin gaba daya ta gama tsara yadda zata kawo karshen kyakkyawar rayuwar da Musaddik yake shimfidawa.Don haka Ta yi tunanin hada auran Musaddik da 'yar kanwarta Hannatu da suke zama a birnin tarayya Abuja, ta bukaci ta dawo nan Minna gunta da zama tunda ta; gama makaranta zaman banza kawai take yi.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM