Page 101
Amma kafin Hannatun ta dawo , sai da Haj kilishi tayi magana da Kanwarta Hajiya Kubra, wacce kusan halinsu daya, don haka koda ta gaya mata kudurinta na hada Musaddik da Hannatu aure da dalilinta, ba ta ji darr! Ba, ta amince, domin tana ganin duk Karuwarsu ce. Hannatu za ta zama musabbabin kusanta su da arziki, ta umarci Hannatu da ta tafi minna,don haka Hannatu ta tarkata kayanta ta yi minna.
Gargadì na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi mata, shine kada ta sake ta dora ma Kanta son Musaddik, domin ta sa a ranta aure ne za su yi na wucin gadi, na dan lokaci, sai ga shi Kuma anyi sa'a Musaddik din burge Hannatu kawai yake yi, amma babu sonsa ko kwayar zarra a zuciyarta. Sai dai ta ci-gaba da shishige masa tare da nuna masa kauna da kuma kokarin nuna masa ita yarinya ce ta-gari, kamar yadda Haj kilishi ta nuna mata, sai dai ko kadan Musaddik bai taba sa ma ransa wai zai so Hannatu ba Ko kurna tana yin abinda take yi masa, don ya so ta ne. Tsawon lokaci Hannatu ta share a gidan, amma Musaddik baya ko bi ta kanta, hidimarsa kawai yake yi. Hakan kuwa ya fara tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, ta rasa mafita, don haka ta nemi aminiyarta Hajiya Rakiya, domin neman shawarar yadda za'a bullo ma lamarin, ba tare da wani dogon tunani ba.