Page 102
Hajiya Rakiya ta bada shawarar a hada Lamarin da Malamai, domin a hada soyayyar Musaddik da Hannatu ta karfi da yaji, wannan shawara ta yi dai-dai da tunanin Hajiya Kilishi don haka ta bukaci rakiyar Hajiya Rakiya zuwa wajen amintaccen bokanta Wato Mai Rakwacam, suna isa tun kafin su fadi abinda ya kawosu. Mai Rakwacam ya gaya masu dalilin zuwansu, ya kuma tabbatar masu da cewa auran Musaddik da Hannatu tamkar an yi, an gama ne. Ya yi ta surkullen ayyukansa, daga bisani ya ba ta kwallin da Hannatu za ta sanya a idanunta,wanda suna hada ido do Musaddik Shi kenan, sai turare da za ta shafa a jikinta,wanda so ake kawai ya ji kamshin, sai kuma wani garin magani da za ta zuba masa a cikin abincinsa da zaran ya ci abincin shikenan bukata ta gama biya. Bayan dawowarsu daga wajen Mai Rakwacam ne. Hajiya Kilishi ta ba Hannatu duk abubuwan da za ta yi amfani da su. Na sawa a abinci kuwa da kanta take sanya masa, kuma sai ta tabbatar ya ci, sannan take barin wajen, kwanaki uku kacal! Tsakani. Musaddik ya haukace akan soyayyar Hannatu. Bai sami sukuni ba, sai da ya gaya mata, ta kuma amince. Da kansa ya sami Alhaji Mansur ya gaya masa ya sami matar aure, wato Hannatu. Alhaji Mansur ya karbi maganar babu yabo, ba fallasa, don dai a so samunsa ne, ya sami wata wacce ba ta da alaka