Musabbabi Book 1

Page 103

by @yargidanimam

da Hajiya Kilishi. Domin baisan dalilin da yasa ya ji kwata kwata bai samu wata natsuwa ba da jin zabin musaddik duk da baida wani buri da ya wuce na musaddik din ya fito da matar aure ya yi masa .Amma tunda abinda dansa yake so, shi yake so, ya sa ya amshi zabin na sa hannu biyu ba tare daya bari ya gane zabin na sa bai yi masa ba.

Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ta sami jindadi, farin-ciki da kuma natsuwa, domin hakanta ya kusa cimma ruwa, nan da nan aka shiga shirye-shiryen biki kasancewar Hannatu marainiya ce mahaifinta ya rasu, kuma zuwa wannan lokacin ba su da komai sai gidan da suke ciki a Abuja shine kadai rufin asirinsu bayan haka basu da wani abin da zasu yi tunkaho da shi. Hakan ne ya sa Alhaji Mansur ya dauki nauyin komai na dakinta da abinda za’ayi mata. Haj kilishi kuwa marairaicewa ta yi ta na yi masa godiya, tana kuma nuna masa tamkar bata damu da auren ba tamkar bata so, don ta nuna don dai kawai musaddik din ya matsa ya na sonta ne ba don haka ba ai Musaddik ya fi karfin Hannatu. Sabida tsabar makirci.

A ranar da Musaddik ya je ya gaya ma Inna Halima, Hannatu ya zaba a matsayin matarsa ta yi masa fatan alheri tare da sanya ma lamarin albarka.duk da acan kasan zuciyarta itama tana jin tamkar danta musaddik bai dace da Hannatu ba, amma alokacin da ya kawo mata ita har gida ta gaisheta sai ta ji ta yaba da hankalinta da nutsuwarta saboda nuna mata tayi duk duniya babu wanda ya kaita ladabi da biyayya da kuma son Musaddik din. Hakan yasa inna Halima ta watsar da wancan tunanin nata, ta yarda da Hannatu.

Daga bisani musaddik ya je gidan kawunsa Malam Mahmud domin shi ma ya sanar da shi maganar auren nasa da Hannatu., a ranar ya tarar da Afrah tana wanke-wanke cike da mutuntawa ta gaishe shi. Ya amsa cikin nuna yabawa da lamuranta. Domin dai duk cikin *ya yan Kawunsa, babu yarinyar da haka nan yake ganin girmanta tare da kaunar dabi ‘unta irin Afrah, yarinyar gaba daya rayuwarta daban ce, ba ta da hayaniya. Bayan ya gaisa da Kawunsa da Mama Hauwa yake sanar da Malam Mahmud maganar Hannatu Malam Mahmud ya yi murna, ya kuma sa albarka sabanin Mama Hauwa da ta hade girar sama da ta kasa, idan ranta ya yi dubu, to ya baci, ta dubi Musaddik tace “Amma Musaddik ca na ke soyayya ka ke da Sakina?”