Musabbabi Book 1

Page 104

by @yargidanimam

Ji Musaddik ya yi saurin kallonta ya ce Cike da mamaki yace”Soyayya, kamar yaya?" Ta ce "Irin yadda na ga taku ta zo daya, sai na ke zaton ko soyayya ku ke yi, ka ga shikenan tuwona, maina, sai ayi hadin zumunta kawai" Musaddik ya girgiza kai ya ce “Mama Hauwa kin fahimta a bai-bai, domin gaskiya ba soyayya muke yi ba. Asalima ni ban taba dasa ma kaina tunanin zan so-ta ba, daya wuce ina sonta amma soyayya ta 'yan-uwantaka. Hannatu dai ita ce na ke son na aura, ita nake kwadayin ta zama abokiyar rayuwata”. Mama Hauwa ta yi turus! Tana kallonsa Cike da takaici, a yayin da Mallam Mahmud ya ce "Kyaleta ka ji, neman zance ne da ita kawai. Musaddik Allah ya sanya alheri, ya sa Hannatu abokiyar arzikinka ce, ya kawo zaman lafiya a tsakaninku”

Cike da girmamawa Ya amsa da "Amin" Daga nan ya zaro kudi ya aje masa, Mallam Mahmud ya yi godiya, kamar yadda ya saba.sannan ya tashi zai tafi, dai-dai inda Afrah take, ya tsaya ya dakko kudi masu yawa ya ba ta, ganin irin kallon wulakancin da Mama Hauwa ke yi masa, ya sa ya fice ba tare da ya bata ko sisi ba. Kamar mama Hauwa na jiran musaddik ya fita kawai ta kafama mallam mahmud gwanjon bala'i, wai yana da damar da zai sa Musaddik ya auri Sakina, amma ya ki sa baki, illa ma goya masa bayan auran Hannatu da yake yi. Daya gaji da sababi da bala'inta ne ya kakkabe rigarsa ya tattara ya bar gidan.