Musabbabi Book 1

Page 105

by @yargidanimam

Bayan auran Hannatu da Musaddik, a Katafaren gidan da Alhaji Mansur ya ba shi ya tare, babu Wanda baya sha'awar rayuwar Musaddik. Allah ya rufa masa asiri, amma baya wulakanci. Baya kyamatar talaka, ga taimako da son shiga duk abinda zai daukaki addini, ba Alhaji Mansur kadai yake yaba da halayen dansa ba, har sauran jama"a suna matukar ganinsa da kima da daraja, domin dai Allah ya tabbatar da natsuwa a cikin rayuwarsa. Musaddik Mansur musaddik kenan. Wadannan halayen nasa da jefa shi a cikin sahun mutanen kirki da kowa yake yi, da kuma alfahari da mahaifinsa yake yi da shi, ya na matukar bakanta ran Haj kilishi ji take kamar ana fisgar ranta.

Duniya ba matabbata ba. Watanni biyu kacal Da auran Musaddik. Allah ya dauki ran jigo kuma gatan Musaddik, wato Alh. Mansur, ya yi rasuwar farat daya a dalilin hadarin mota a hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja, domin halartar wani taron yan kasuwa da suka gayyace shi. Sai gawarsa ce ta dawo Minna, inda a nan ne aka yi masa suttura aka rufe shi. Fadin tashin hankali da kuncin da Musaddik ya shiga, bata lokaci ne. Nan da nan ya rame, ya fige, ya fita hayyacinsa. Rasuwar mahaifinsa ta yi Mummunan taba shi, hatta abinci baya iya ci. Duk wani me imani, dole ya tausaya masa, domin ya fada mawuyacin hali.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM