Page 106
Haka Inna Halima da Malam Mahmud su ka yi ta Kokarin dawo da shi musaddik hayyacinsa tare da yi masa addu'ar samun dangana. Ita kam Hajiya Kilishi duk da rasuwar mijin nata ya taba mata zuciya, to fa maganar abinda ya mutu ya bari, ya fi damunta, bakin-cikinta daya ne na kaso mafi tsoka da Musaddik zai samu, domin dai ta san kason 'ya' yanta mata biyu. MusaddiR zai ci shi kadai.
Idan da akawi abinda za ta fi shi da shi, bai wuce tumunin takabarta ba da kason 'yarta daya, ta san kuma babu abu daya da 'ya'yanta zasu bari a hannunta, tunda sun riga sun mallaki hankalinsu. Suna kuma tare da mazajensu, don haka ta san da kasonta kadai za ta tashi, shin ya za ta yi? Ta san dai ba ta da damar hana Musaddik gadonsa, domin ya san yancinsa. Yasan abinda musulunci ya tanadar masa.
Abinda ko take gudun ne ya faru, domin bayan fitarta takaba, aka yi rabon gado, ba gidan Musaddik ba motarsa ba kuma kamfaninsa na siminti a cikin rabon Domin Alhaji Mansur ya rubuta a rubuce cewar duk wadannan abubuwan ya ba shi su kyauta ne. Hakan ko ya tada hankalin Hajiya Kilishi, domin zahiri wannan karon Alh mansur ya yi son rai don kamata ya yi yadda ya ba musaddik wannan tarin dukiyar ace su ma su Hassana ya basu domin su ma yayansa ne, amma soyayyar musaddik ya makantar da shi daga ganin illar wannan bambancin da yake nunawa a tsakanin yayansa, wanda kusan shine dalilin da ya jefa rayuwar gudan jininsa cikin gararin rayuwa bayan rasuwar tasa, domin dai Haj kilishi ta kara haukacewa da tsanar musaddik fiye da kullum, domin duk akasafin rayuwarta babu abinda take hangowa sai gado, duk da babu wanda yasan gawar fari,
To ga dai abu a rubuce, balle ta ce karya ne ta kuma danne , babu wannan damar Sannan da aka yi rabon gadon Musaddik ya tashi da kaddarori da Kudade makudai amma duk ba su a gabansa, ba su kuma burge shi ba, ya fi