Page 107
bukatar mahaifinsa fiye da komai a duniya, ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa gaba daya tunaninta ya tafi ne akan dukiyar Musaddik da tunanin yadda dukiyar za ta zama nata, watau ta mallake ita daya.
Abu na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi, shi ne kokarin mallake Musaddik, da taimakon Bokanta Mai Rakwacam, ta kashe makudan kudi Kafin bukatarta ta biya, domin kuwa ta sami mallake Musaddik, komai zai aikata ko zai zartar akan duk abinda ya shafi rayuwarsa sai da saninta, sai da kuma amuncewarta Yana matukar jin tsoronta tare da tsoron bata mata rai, sai daya zamana duk duniya Musaddik gani yake baida kowa sai Hajiya Kilishi, hatta dangantakarsa da su Inna Halima duk ta ja baya, domin ko kafin ya je gidanta ma aiki ne. Kwata kwata ya dauke kafarsa basa ganinsa wanda hakan ba karamin ta da hankalin su ya yi ba.A yayin da Hannatu take tsiro da halayen wulakanci da musgunawa ga musaddik sam ba ta ganin mutunci ko darajarsa mutuncin ko darajarsa.abu kadan tun bayan rasuwar Alh mansur zata hau cin mutuncinsa. Gaba daya duk ta canja.
yayin da shi kuma musaddik din ya dora ma kansa tsoronta da shakkarta, gaba daya lamuran Musaddik suka dagule, rayuwarsa ta shiga cikin gigita da dimauta. Wannan shine tushen fara lalacewar rayuwar musaddik.
Domin dai baida tunani nasa na kansa, sai wanda Hajiya Kilishi da Hannatu suka tusa masa, haka zalika baida ta cewa, sai cewarsu,