Musabbabi Book 1

Page 108

by @yargidanimam

A hankali Hajiya Kilishi da Hannatu suka fara karar da dukiyar Musaddik,ya zama wanda da sun ce,ya yi kaza bai samun sukuni, sai ya aikata masu, Haka Hajiya Kilishi ta yi ta sa Musaddik yana sa hannu akan Kadarorinsa me tabbatar da cewa ya mallaka mata, wasu kuma ya mallaka ma Hannatu. Daga Inna Halima har Malam Mahmud babu wanda ya san wainar da ake toyawa, balle su taimaka masa su yi ma tufkar hanci tun nesa sa kofa .Hatta kamfanin ya daina zuwa kullum yana gida, hakan ko ya fi komai yi ma Hajiya Kilishi dadì, inda ta fara tura Hannatu kamfanin tana shiga ofis dinsa hakan ko ya janyo cece ku ce a kamfanin a tsakanin ma'aikatan, daga bisani Hajiya Kilishi tasa Musaddik ya yi ma ma'aikatansa bayanin cewa Hannatu ce za ta ci-gaba da daukar nauyin kamfanin, domin shi ayyuka sun yi masa yawa Sannu a hankali cikin dabara da kauce hanyar Allah ta bin Bokaye da Hajiya Kilishi ta saba ta sami nasarar kwace kamfanin daga hannun Musaddik, inda ya sa hannu aka kuma kafa shaidu akan cewa ya bar ma natarsa kamfanin halas-malak. Wanna lamari ya daga hankalin abokin Masaddik kuma (Cashier) na kamfanin Murtala domin zuwa wannan lokacin ya fara zargin tamkar Musaddik baya cikin hankalinsa, domin abubuwan da suke faruwa abubuwa ne masu matukar daure kai matuka. Akwai alamar tambaya domin hatta mu’amalar Musaddik da mutane duk ta canja. Yana yin abubuwa tamkar bai san abinda yake yi ba.