Musabbabi Book 1

Page 109

by @yargidanimam

Da kansa ya sami Musaddik ya tunantar da shi muhimmancin kamfanin a gare shi, ya kuma tambaye shi meye dalilinsa na barin ma matar da bai taba koda haihuwa da ita ba irin wannan dukiya? Anya kuwa yana cikin hayyacinsa. Musaddik ya numfasa yana kallon Murtala, sannan yace cikin wata irin fuska “Ni fa babu abinda ke gabana, ko Yake min dadì gaba daya rayuwar ma ni ta fita kaina, don haka duk wata dukiya, ni ba ta gabana. Kuma Hannatu matata ce, ko ta haihu ko ba ta haihu da ni ba, zan iya yi mata kyauta, saboda haka don Allah ka tsaya a matsayinka na aboki na, ka daina kokarin shiga abinda bai dameka ba,” Haka Murtala ya bar Musaddik cike da mamakin irin maganganun daya gaya masa, domin dai ya san ba haka Musaddik yake ba a da don haka bai ji haushi ba. Ya yi alkawarin zai ci-gaba da fahimtar da shi illar abinda yake aikatawa, har ya fahimta, ko ya nemi wani shakikin Dan-uwansa ya sanar da shi abinda ke faruwa ko za su iya taimakawa.

Sai daya zamana Hajiya Kilishi ta gama zare komai, domin hatta gidan da yake ciki, ya mallaka shi ga Hannatu, sannan har zuwa wannan lokacin babu abinda bangaren dangin Musaddik na wajen uwa suka sani.a lokacin ne Hajiya Kilishi ta ga ya kamata ta dauki mataki na karshe na karasa lalata rayuwar Musaddik.