Page 110
Domin ba ta kaunar duk wani sanadi da Zai sa Musaddik ya farga ya dawo hayyacinsa, ya fahimci irin mummunar barnar da ta yi ma rayuwarsa, ko kuma hankulan mutane da na dangin mahaifiyarsa su ankara da halin da ta jefa Musaddik. Don haka ta fara neman shawarar aminiyarta Hajiya Rakiya yadda za su yi da Musaddik. Hajiya Rakiya ta yi shiru tana nazarin lamarin, a nan ne Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce "Ni fa Hajiya Zuciyata a bushe take akan Musaddik ko kadan ba na kaunar yaron nan, musamman idan na tuna ni fa ba ni da da namiji, sannan ga irin fifikon da ya samu sama da nawa yayan, sannan wannan daraja da natsuwa da yake da shi da kowa ke sha’awar sa ya na matukar bata min rai,sai na ji tamkar na raba Musaddik da doron Kasa" Ta dan hadiye yawu gami da kallon Haj Rakiya da take sauraron ta, sannan ta ci-gaba da cewa cikin wata muguwar Fuska, da gaba daya ta canja yanayin ta, ta koma tamkar ba ita ba. "Kamar yadda a yanzu na gama tunanin lokaci ya yi da zan raba Musaddik da duniya gaba daya, domin duk wani amfani da zai yi min, ya riga ya gama yi min, kuma ina ganin mutuwarsa ita ce kadai hanyar da asirina zai rufu akan dukiyarsa, domin babu wanda zai tuhumeni..” Hajiya Rakiya ta yi gaggawar dakatar da ita tana yi mata kallon ko kin haukace ne? Ta ce "Haba Hajiya. Shin rashin imaninki har ya kai ki fara tunanin daukar rai, bayan duk irin ta'asar da ki ka yi masa na raba shi da arzikinsa mallakarsa, da raba shi da yancin zama miji me cikakken iko a gidansa.duk wannan bai isa ba, sai kin kashe shi?
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM