page 111
abin ya yi yawa gaskiya, kuma ni ban goyi bayan wannan shawarar ta ki ba na a kashe shi, saboda babu komai a cikin shawarar taki sai gagarumin hatsari Shin ba kya ma tunanin ko Musaddik ya rasu yan-uwan mahaifiyarsa za su iya bin kadin dukiyar musaddik din daya mallaka miki, ba gara kin bar shi araye, shi ya gaya ma duniya da kowa ma cewa shi ne ya mallaka maku dukiyar ba. Idan ko mai kaya ya ce ya bayar, to waye ya isa ya ce bai bayar ba? Idan kuma ki na tunanin shi zai iya yi miki bore wata rana ne, ai akwai wata hanyar da ta fi wacce ki ke son bi saukin bi."Haj kilishi cike da gamsuwa da maganganun Hajiya Rakiya ta ce "Wace. hanyar ce?" Hajiya Rakiya ta ce "Ba sai a lalata rayuwarsa ba, a raba shi da kyakkyawan tunani, a hana shi shiga cikin mutanen kirki, balle har shawarwarinsu su yi tasiri wata ran a rayuwarsa. Me zai hana a kwace kwarjini da kamalar da jama"a suke ganinsa da ita, ina nufin a hada shi da shaye-shaye, domin shaye-shaye shine tushen lalacewar rayuwar, duk wani matashi. Shine kuma zai zama abin kyama a wajen mutanen kirki “ Ta gyara zama tana kallon aminiyarta cike da jindadin maganarta da jin shawarar ta ta itace abar dauka ta ce “ ina jinki Haj”
Hajiya Rakiya ta ci-gaba da cewa, "Kin ga kuma mutane ba za su taba zarginki ba, za su dauka don dukiyar da aka bar masa ne ya sa ya canja halinsa da kuma bakin-cikin rashin mahaifinsa,